Babu tabbacin mutuwar shugaban Amurka Donald Trump–The Royal News English

0
15

An samu bazuwar jita-jita a kafafen sada zumunta da ke cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya mutu, inda aka yi amfani da kalmomin “Trump is Dead” da “HES DEAD” a matsayin taken da ke ta yawo a dandalin X.

Rahotanni sun nuna cewa an wallafa bidiyo da hotunan da ba a tabbatar da sahihancin su ba, inda aka nuna motar asibiti a gaban Fadar gwamnatin Amurka ta White House. 

Wannan ya ƙara rura wutar maganganun, sai dai babu wata hujja ta gaskiya da ke tabbatar da cewa Trump ya rasu.

Wasu kafofin sun danganta barkewar jita-jitar da hirar da Mataimakin Shugaban ƙasa JD Vance ya yi, inda ya ambaci batun gadon shugabanci a cikin wata tattaunawa da USA Today. 

Haka zalika, an kuma danganta maganar da shirin barkwanci na The Simpsons ya yi a taron San Diego Comic-Con, wanda aka yi amfani da shi wajen kirkirar bidiyoyin karya a TikTok.

A baya-bayan nan, Trump ya yi fama da matsalar lafiyar jijiyoyi, wadda likitoci suka bayyana a watan Afrilu, duk da cewa rahoton lafiyar sa ya nuna cewa yana cikin koshin lafiya.

Duk da haka, babu wata majiyar gwamnati da ta tabbatar da cewa Shugaban ya rasu. 

Hotunan da ake yadawa sun kasance jita-jita ne kawai da ba su da tushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here