Wani jigo a jam’iyyar APC, Farouk Adamu Aliyu, ya bayyana cewa mafi yawan al’ummar Arewa za su ci gaba da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaben 2027.
Aliyu ya yi wannan bayani ne a ranar Juma’a yayin hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta Arise, inda ya ce babu wani babban dan adawa da zai iya kalubalantar Tinubu a zaben da ke tafe.
“Mafi yawan mutanen Arewa za su zabi APC, kuma Tinubu zai sake tsayawa takara. Mun girmama tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, haka nan Atiku Abubakar da sauran shugabannin Najeriya, amma a halin yanzu ban ga wanda zai iya fafatawa da Tinubu ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa ikon zaben shugaba a hannun talakawa yake, ba na wasu ‘yan siyasa kawai ba.
Duk da cewa akwai wasu da ke nuna rashin jin dadin su da gwamnatin yanzu a Arewa, Farouk ya jaddada cewa APC na nan da karfin goyon baya daga mafiya yawan jama’a.