Babban Editan BBC Hausa ya musanta zargin cin zarafi a wurin aiki

0
13

Shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, ya karyata zargin cin zarafin ma’aikatan sa a wurin aiki da aka danganta masa bayan wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta.

A bidiyon, tsohuwar ma’aikaciyar BBC Hausa, Halima Umar Saleh, ta bayyana cewa ta fuskanci tsangwama daga wani babba a ofishin, wanda hakan ya jefa ta cikin damuwa da kuka akai-akai. Sai dai duk da haka ba ta ambaci sunan kowa ba yayin zantawar.

Sai dai daga baya wasu sun fara nuna yatsa kan Tanko, wanda ya ce zargin ba gaskiya ba ne.

 Tanko ya tabbatar da cewa ya yi murabus daga aikin sa, amma bai yi bayani dalla-dalla kan dalilin hakan ba.

BBC dai ba ta fitar da sanarwa kai tsaye kan lamarin ba zuwa yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here