Gwamnatin tarayya ta amince da manyan ayyuka a jihar Lagos da kudinsu ya kai Naira 3.9 tiriliyan cikin shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wannan adadi ya fi jimillar abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas tare, waɗanda suka samu Naira triliyan 3.56.
Manya daga cikin ayyukan da aka amince da su a Lagos sun haɗa da gyaran filin jirgin sama na Murtala Muhammed akan Naira biliyan 712, ginin gadar Carter akan Naira 359, aikin gina bakin teku a Ebute-Ero a Naira biliyan 176, da kuma babban titin gabar tekun Lagos-Calabar na sama da Naira triliyan 1.6.
Sai dai wannan ya jawo cece-kuce daga kungiyoyi da ‘yan siyasa da ke zargin gwamnatin Tinubu da fifita Lagos da yankin Kudu maso Yamma a kan sauran sassan ƙasar.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya musanta zargin, inda ya ce rabon ayyukan ya kasance daidaito a dukkan jihohi karkashin shirin Renewed Hope Agenda.
Masu sharhi sun bayyana cewa Lagos na da muhimmanci a tattalin arzikin Najeriya da Afirka ta Yamma, amma hakan bai kamata ya hana sauran yankuna samun hakkinsu na ci gaba ba.