Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 14, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Maryam Sabo, ta yanke hukuncin daurin shekaru 21 ga wani malamin makarantar Islamiyya mai suna Nasif Sha’aibu, bayan ta same shi da laifin fyade da kuma lalata wata yarinya ‘yar shekara tara, wadda dalibar sa ce a makarantar Islamiyya.
A zaman kotun, lauya mai gabatar da ƙara, Barista Fa’iza Dahiru Sidi, ta gabatar da shaidu guda biyar da suka tabbatar da zargin. A gefe guda, Barista Aminu Umar, shi ne ya tsaya a matsayin lauya mai kare wanda ake tuhuma.
Bayan kotun ta gamsu da shaidun da aka gabatar, ta yanke wa wanda ake tuhuma hukunci kamar haka:
Shekaru 14 a gidan gyaran hali kan laifin fyade.
Shekaru 7 a gidan gyaran hali kan laifin lalata yarinya.
Biyan tarar ₦200,000.
Biyan diyya ₦50,000 ga yarinyar da aka ci zarafi.
Tun shekarar 2022 aka fara zargin Nasif Sha’aibu, da aikata wannan mummunan laifi, lokacin da yake koyar da ɗalibar a wata makarantar Islamiyya da ke unguwar Mariri, cikin karamar hukumar Kumbotso, Jihar Kano.