Matashi ya fasa wa matar babansa ido kan awara a Kano

0
7

Wani matashi mai suna Najib Aminu, mazaunin Kwanar Dala a Kano, ya shiga hannun jami’an tsaro bayan ya lakada wa matar babansa, Maryam Ibrahim, duka har ta rasa ido ɗaya, sakamakon rigimar sayen awara.

An gurfanar da Najib a gaban Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba ɗaya da ke Kofar Kudu, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Shamsuddin Ado Abdullahi Unguwar Gini.

Rundunar ‘yan sanda ce ta kama shi bisa zargin aikata laifin razanarwa da kuma haddasa rauni mai tsanani.

A gaban kotu, lauyar gwamnati, Barista Aliya Aminu Yar Gaya, ta karanto masa tuhumar. Najib ya musanta tuhumar razanarwa, amma ya amince da laifin duka da aka ce ya aikata wa matar babansa.

Mai shari’a ya kafa masa shaidun ikirari, sannan ya tura shi gidan gyaran hali har zuwa ranar 15 ga Satumba, 2025, domin yanke hukunci.

Rikicin ya samo asali ne lokacin da Maryam Ibrahim ta tura kanin Najib sayen awara, lamarin da ya fusata shi, inda ya kai mata hari da duka, wanda ya janyo ta rasa idon hagu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here