Shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, Bayo Ojulari, ya bayyana cewa rayuwarsa da ta wasu jami’an gudanarwa na kamfanin na cikin barazana saboda gyare-gyaren da ya kawo a bangaren man fetur da iskar gas.
Ojulari ya ce wasu masu ƙarfi a masana’antar suna ƙoƙarin ganin an sauke shi daga mukamin sa saboda matakan da ya ɗauka na farfaɗo da matatun mai, bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi tawagar ƙungiyar ma’aikatan fetur da iskar gas PENGASSAN, karkashin jagorancin Festus Osifo, a ofishinsa da ke Abuja.
Bayo, ya ƙara da cewa akwai shirin amfani da tsarin NLNG wajen dawo da matatun mai su fara aiki da cikakken ƙarfin su. Duk da barazanar da yake fuskanta.
Ojulari ya ce yana da niyyar ganin matatun mai sun fara aiki yadda ya kamata.
“Ba ni da wani abu da zan ɓoye wa kowa. Ni ba ɗan siyasa ba ne, amma zan koyi dabarun siyasa idan ya zama dole. Babban buri na shi ne a tabbatar matatun fetur namu sun dawo aiki” in ji shi.