Miji ya kashe matar sa da duka saboda rashin zuwa gona a kan lokaci

0
36

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ekiti ta tabbatar da mutuwar wata mata mai suna Ofone Modupe Alasin, a garin Efon-Alaaye, bayan zargin cewa mijinta ya lakada mata duka har lahira.

Kakakin rundunar, SP Sunday Abutu, ya bayyana cewa an kama mijin mamaciyar yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan matar ta ki zuwa gona a kan lokaci, abin da ya fusata mijin ta ya dinga bugur ta har ta mutu.

Wani makwabcin gonar su ya ce ya jiyo ihun matar tana neman taimako, amma mijin ya ci gaba da dukan ta.

Bayan haka, an ruwaito cewa mutumin ya tilasta wa matarsa ta tafi debo masa ruwa daga wani rafi, amma a hanya jikinta ya yi rauni ta fadi ta mutu.

Rundunar ’yan sanda ta ce bincike na ci gaba, yayin da ake tsare da wanda ake zargi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here