Za mu raba sabbin katunan zaben da aka yi rijista —INEC

0
108

Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC ta bayyana cewa a cikin watan Nuwamba mai zuwa ne duk waɗanda suka yi sabuwar rajista za su karɓi katunan su na je fa ƙuri’a.

Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wani babban taro da ya halarta, wanda ya gudana a birnin Washington DC da ke ƙasar Amurka, inda ya bayyana cewa kashi hamsin cikin ɗari na waɗannan katuna suna nan, amma ba a riga an tura su wuraren da za a karɓa ba.

Haka kuma, a cikin jawabin nasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa Hukumar tasa ta soke rajistar mutum miliyan 2.7 waɗanda aka samu sun yi rajista fiye da sau ɗaya.

Shugaban ya kuma nuna matuƙar damuwar sa bisa rashin tsaro da ya addabi sassan ƙasar nan, wanda yace ba ƙaramin tasgaro ba ne ga hukumar.

Ya ce, wannan abu daɗaɗɗe ne, amma abin damuwar ita ce, a da wani ɓangare ne na ƙasar ke fama da rashin tsaron, wato yankin Arewa maso Gabas, amma yanzu abin ya zama ya watsu zuwa ko’ina.

“Amma dai muna nan mun sanya idanun mu, musamman a yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas na ƙasar nan. Domin mutane ne fa ke gudanar da zaɓen nan,” inji shi.