PDP ta bawa Tinubu damar komawa shugabancin ƙasa–Dele Momodu

0
1

Dan siyasa kuma ɗan jarida, Dele Momodu, ya caccaki jam’iyyar PDP bisa matakin da ta dauka na tsayar da ɗan takarar shugaban kasa na 2027 ga kudu, yana mai cewa hakan kyauta ce kai tsaye ga shugaba Bola Tinubu domin komawa mulki a wa’adi na biyu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Momodu ya ce PDP ta “sauka daga tasirin ta, sannan ta amince da matsin lamba marar amfani” daga wasu ‘yan jam’iyyar da ya zargi da yin aiki da jam’iyyar APC mai mulki.

Ya danganta wannan mataki da tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yana mai cewa shiri ne na taimaka wa Tinubu wajen lashe zabe a 2027. “Duk mai hankali ya san cewa wannan aikin Wike ne amma muryar Tinubu. Shirin su ba boyayye ba ne,” in ji shi.

Momodu ya kuma zargi PDP da cin amanar ‘ya’yanta a jihar Ribas da kuma barin Gwamna Siminalayi Fubara a lokacin rikicin siyasa. Ya tunatar da yadda Wike ya ki amincewa da tsarin rabon mulki a 2022, har ya nemi kujerar mataimakin shugaban kasa tare da dan takara daga arewa, amma yanzu shi ke tsayawa a kan cewa mulki sai ya koma kudu.

Haka kuma, ya karyata jita-jitar cewa ana iya tsayar da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Peter Obi ko gwamnan Oyo, Seyi Makinde, a matsayin ‘yan takara, yana mai cewa hakan “ƙarya ce tsagwaron karya.”

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!