Mutane 14 sun jikkata a hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna

0
8

Rahotanni sun tabbatar da cewa wani jirgin ƙasa da ya taso daga tashar Kubwa a Abuja zuwa Kaduna ya yi hatsari a kusa da tashar Asham, lamarin da ya jawo tsoro da tashin hankali ga fasinjoji.

Aƙalla mutum 14 ne suka jikkata a wannan hatsari, inda aka garzaya da su cibiyar kiwon lafiya ta Idah a ƙaramar hukumar Kagarko, Jihar Kaduna, kafin daga bisani a tura su zuwa Kaduna don samun karin kulawa.

Hukumar kula da jiragen ƙasa ta ƙasa (NRC) ta sanar da dakatar da dukkan ayyukan jirgin Abuja–Kaduna har sai an kammala bincike. Shugaban hukumar, Kayode Opeifa, ya bayyana cewa ana gudanar da bincike tare da haɗin gwiwar Hukumar Tsaro ta NSIB da sauran hukumomi domin gano musabbabin hatsarin. Ya kuma tabbatar da cewa an fara mayar wa da fasinjoji kuɗin tikitin da suka saya.

Hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA ta tabbatar da cewa babu wanda ya rasu a hatsarin, sai dai mutane da dama sun samu raunuka. 

Shima Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwarsa kan faruwar lamarin, inda ya ce ko da yana kan tafiya a ƙasar Brazil yana karɓar rahotanni kan lamarin. Ya yi alƙawarin daukar matakan da suka dace don hana maimaituwar irin wannan hatsari a nan gaba.

Wannan ba shi ne karo na farko da jirgin Abuja–Kaduna ya yi hatsari ba. A shekarun baya dama, an sha samun hatsarin a kan wannan hanya, haka kuma a shekarar 2022, ‘yan ta’adda sun kai hari kan jirgin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, da kuma sace wasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here