Malaman jami’a mambobin kungiyar ASUU reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK) sun gudanar da zanga-zanga a ranar Talata kan kin biyan su albashin da suka samu karin matsayi da sauran hakkokin jin dadin ma’aikata.
Kungiyar ta bayyana cewa gwamnati ta gaza cika alkawuran da ta dauka kan al’amuran walwalar malamai, lamarin da ya tilasta musu fitowa domin bayyana damuwarsu.
Malaman sun ce yanayin da gwamnati ta sanya su a ciki ya kawo koma bayan harkokin koyarwa a jami’o’in Najeriya.