Hukumar kula da harkokin man fetur na kan tudu (NUPRC) ta bayyana cewa samar da ɗanyen man fetur a Najeriya ya karu da kaso 0.89 cikin 100 a watan Yuli 2025, inda ake haƙo ganga miliyan 1.71 a kullum.
Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce wannan ya hada da ganga miliyan 1.50 na danyen mai da kuma ganga dubu 204,864 na sauran mai da ya danganci iskar gas.
Idan aka kwatanta da watan Yuli na shekarar 2024, an samu karin kaso 9.9 cikin 100, daga ganga miliyan 1.56 zuwa 1.71.
Daga cikin tashoshin samar da danyen mai, Forcados ya fi kowanne da ganga miliyan 9.04, yayin da Bonny terminal ya samar da ganga miliyan 8.07 karin kaso 12.7 cikin 100 daga watan da ya gabata.
Haka kuma, tashoshin Escravos, Bonga, Odudu da Brass suma sun samu karin yawan samarwa, inda tashar Brass ta fi da kaso 27 cikin 100.
Majalisar kasashen dake da arzikin mai ta duniya OPEC ma ta tabbatar da cewa matsakaicin samar da man fetur na Najeriya ya kai ganga miliyan 1.50 a kullum a watan Yuli.