Gwamnatin Tarayya Tayi Gargadin Samun Ambaliya A Jihohin Arewa 9

0
1

 Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta hannun Cibiyar (FEW Center) ta sake fitar da sabon gargadin ambaliya ga wasu jihohi tara a arewa sakamakon hasashen ruwan sama mai yawa daga 25 zuwa 29 ga watan Agusta, 2025.

A sanarwar da Daraktan Sashen Kula da Ambaliya da Gabar Teku, Usman Abdullahi Bokani, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa wasu garuruwa a jihohin Adamawa, Katsina, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Sokoto, Zamfara da Borno na iya fuskantar ambaliya.

Jihohin Adamawa da Katsina sune suka fi shiga cikin barazanar, inda aka ambaci garuruwan Mubi, Shelleng da Abba-Kumbo (Adamawa) da kuma Katsina, Kaita da Bindawa (Katsina).
Haka kuma, an sanya garuruwan Sumaila (Kano), Gwaram (Jigawa), Nafada (Gombe), Ngala (Borno), Anka (Zamfara), Makira (Sokoto), Azare da Jama’are (Bauchi) cikin jerin wuraren da ke cikin haɗarin ambaliya.

Cibiyar ta bukaci hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a jihohin da abin ya shafa da su dauki matakan gaggawa, tare da bayar da rahoton duk wani yanayi da zai iya tasowa.

A makon da ya gabata ma, cibiyar ta yi irin wannan gargadi ga wasu jihohi bakwai, inda ta umarci al’ummomin da ke bakin kogin Nijar daga Jebba zuwa Lokoja da su fara shirin barin gidajensu saboda karuwar ruwan kogin.


LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!