Ƙungiyar ‘Yan Jarida reshen wakilan kafafen yaɗa labarai ta Correspondents’ Chapel, ta jihar Kano, ta dawo da hidimar amfani da talabijin ta zamani ta hanyar sanya kayan kallo na DSTV a sakateriyar ta, tare da sanya na’urar intanet ta Airtel 5G ODU domin ƙara inganta amfanuwar yanar gizo ga mambobin ta.
Wannan mataki zai taimaka wajen sauƙaƙa samun labarai kai tsaye, al’amuran yau da kullum, abubuwan da ke faruwa a duniya, da kuma sahihin bayanai daga yanar gizo ga ƴan jarida masu ruwaito labarai a jihar.

Da yake jawabi a lokacin kaddamar da shirin, Shugaban Ƙungiyar, Murtala Adewale, ya bayyana cewa wannan yunkuri wani ɓangare ne na shirin shugabancin ƙungiyar na inganta yanayin aiki da samar da kayan zamani da za su taimaka wajen bada rahotanni cikin inganci da sahihanci.

“Jarida tana bunƙasa ne bisa bayanai. A wannan lokaci na samun labarai daga kafafen zamani, kafafen talabijin kamar DSTV na ba da damar samun labarai kai tsaye daga Najeriya da duniya, yayin da yanar gizo mai sauri yake taimaka wa mambobinmu wajen tantancewa, bincike, da tura labarai ba tare da tangarda ba. Wadannan kayan aiki ba kawai don jin daɗi bane, sai dai muhimman kayan aiki ne da ke taimakawa wajen rahotanni masu inganci,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen jin daɗin mambobinta domin ƙara inganta aikin jarida.
Wasu mambobin ƙungiyar da suka tofa albarkacin bakinsu sun yaba da wannan mataki, inda suka bayyana cewa DSTV da yanar gizo mai ƙarfin 5G za su zama manyan hanyoyin samun labarai, tabbatar da sahihancin bayanai, da kuma tattaunawar a tsakanin mambobin.