Asibitin AKTH da Saudiya sun gudanar da tiyatar zuciya kyauta a Kano

0
10

Asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) tare da hadin gwiwar cibiyar jin ƙai ta sarki  Salman, na ƙasar Saudiyya, da kuma cibiyar Al-Balsam, daga Saudi Arabia sun kammala aikin tiyatar zuciya kyauta ga marasa lafiya a Kano.

Shugaban sashen aikin zuciya na AKTH, Dr. Jamil Ismail Ahmad, ya ce wannan shiri ya ceci rayuwar marasa lafiya da ba za su iya biyan kudin jinya a kasashen waje ba.

“Yawanci kudin wannan aiki yana tsakanin Naira miliyan 8 zuwa 10 a Najeriya, kuma sama da Naira miliyan 25 idan aka yi a waje. Amma nan ana yi wa mutane kyauta” inji shi.

Ya kara da cewa ana zaben marasa lafiya ne bisa tsauraran matakai, inda ake fifita wadanda ba su da matsaloli masu tsanani domin tabbatar da nasarar aikin.

Dr. Ahmad ya yabawa hadin gwiwar da Saudiya, yana mai cewa tana taimaka wa wajen horar da likitoci da karfafa ingancin ayyukan asibitin.

Shugaban tawagar Saudiya, Dr. Abdullah, ya bayyana cewa marasa lafiya da dama a kasashe masu tasowa na zuwa asibiti ne bayan cutar ta tsananta, abin da ke kara hadarin mutuwa daga cutar.

Ya ce a Kano sun riga sun yi wa mutane biyar aiki kuma za a yi karin wasu a kwanaki masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here