Gamayyar kungiyoyin Fulani makiyaya a jihar Kano ta kai ziyarar aiki ga Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida ta jihar, domin gabatar da korafe-korafen da suka shafi matsalolin da suke fuskanta a wasu kananan hukumomin jihar.
Jagoran tawagar, Alhaji Ahmad Chanji Mangari, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Kan Allah, ya bayyana cewa sun yanke shawarar gabatar da korafe-korafen ne ta hanyar doka domin neman shawo kan matsalolin da suka hada da cinye burtalai da kuma siyar da filayen kiwo.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda ya samu wakilcin mukaddashin babban sakataren ma’aikatar, Inuwa Idris Yakasai, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta dauki matakan da suka dace wajen warware matsalolin da ake fuskanta tsakanin makiyaya da manoma.
“Ina tabbatar muku cewa za mu isar da wannan korafi ga Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, kuma gwamnati za ta dauki matakan gaggawa don tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar,” in ji shi.
Ya kuma yabawa kungiyoyin makiyayan bisa bin doka da oda wajen gabatar da koke-kokensu ba tare da daukar doka a hannu ba.