Zamu tallafawa manoman rani dubu 15 a Kano ta kudu–Kawu Sumaila

0
8

Sanatan Kano ta kudu, Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, ya sha alwashin tallafawa manoma da inganta harkokin noman rani a yankin da yake wakilta.

Kawu Sumaila, ya bayyana hakan a lokacin da yakai ziyarar duba injinan ban ruwa dubu 5, wanda ya tanada domin rabawa manoman ƙananun hukumomi 16 na Kano ta kudu, da manufar haɓɓaka noman rani ga manoma akalla dubu 15.

Sanatan yace an gina manyan rijiyoyin burtsatse guda dubu 5, da aka tabbatar zasu iya bayar da ruwa ga gonaki dubu 15.

Daga cikin abubuwan da aka tanada akwai injinan ban ruwa da mesar ban ruwa da sabbin rijiyoyi dubu 5, wanda nan gaba kaÉ—an za’a raba su kyauta ga manoman rani a yankin.

Wannan tallafi muna sa ran zai taimakawa Manoma da inganta harkokin noman rani a Kano ta kudu, jihar Kano, arewa da Najeriya baki É—aya, inji Kawu.

Muna kira ga manoma su haÉ—a kai domin kowacce rijiya daya ta bayar da ruwa ga gonaki 3, a cewar Kawu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here