An ceto yaran Adamawa da aka siyar a Anambra akan Naira 800,000

0
1

Gwamnatin Jihar Adamawa ta ce ta ceto yara 14 da aka sace daga jihar sannan aka sayar da su a Anambra a tsakanin Naira 800,000 zuwa N1.7m kowanne yaro ɗaya.

A wani biki da aka gudanar a Yola ranar Laraba, an mayar da yaran hannun iyayensu.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Kaletapwa George Farauta, ta bayyana cewa bayan rahotannin yawan bacewar yara a watan Yuli, gwamnati tare da jami’an tsaro sun kaddamar da bincike wanda ya kai ga cafke wata mata mai suna Ngozi Abdulwahab, wadda ake zargi da jagorantar harkar safarar yara daga arewa zuwa kudu.

An ce matar na amfani da kayan ciye-ciye da kyaututtuka wajen jawo hankalin yara masu shekaru 4 zuwa 9 a unguwar Jambutu, Karamar Hukumar Yola ta Arewa, kafin ta tafi da su zuwa kudu maso gabashin Najeriya inda ake sayar da su.

Gwamnatin ta kuma bawa kowane iyali da aka ceto tallafin Naira 100,000 tare da kayan abinci.

Gwamnatin ta kuma yi alkawarin gurfanar da wadda ake zargin.

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!