Akalla manoma 15 aka kashe a wani sabon hari da aka kai a kauyuka bakwai na yankin Chakfem, a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato. Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Manden, Jibin, Tim, Jiblang, Koppang, Mihdihin da Jilem.
Rahotanni sun ce maharan sun kona gidaje da dama tare da sace dabbobin al’umma, lamarin da ya tilasta wa fiye da mutane 3,000 tserewa daga gidajensu. Rahotannin sun tabbatar da cewa wadanda suka jikkata suna samun kulawa a asibitin COCIN da ke Mwar-Chakfem.
Shugaban kungiyar cigaban Mwaghavul (MDA), Bulus Dabit, ya tabbatar da harin, inda ya ce maharan sun kai hari ne a daren Litinin, lokacin da jama’a ke hutu a gidajensu. Ya ce gidan mai sarautar gargajiyar yankin da motarsa suma an banka musu wuta.
A cewar sa, rashin samun damar shiga kauyukan ya hana jami’an tsaro kai dauki cikin lokaci, inda maharan suka shafe sa’o’i suna aikata ta’asa. Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa domin kare rayukan jama’a.
Wani basaraken yankin, Da Raymond Yombish, wanda ya tsira, ya ce ya bar motarsa ta ofis domin tsira da rayuwarsa, amma maharan sun kona ta.
Sai dai shugaban Miyetti Allah a jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya nesanta Fulani daga harin, yana mai cewa su ma suna jajantawa wadanda abin ya shafa, tare da kira ga jami’an tsaro da su gudanar da bincike.