Ya Kamata Tinubu Ya Rage Kuɗin Hajji da Kashi 50–Sheikh Ƙalarawi

0
1

Fitaccen malamin addinin Islama a jihar Kano, Sheikh Tijjani Bala Kalarawi, ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba kuɗin aikin Hajji na shekara ta 2026 tare da bayar da tallafin kashi 50 ga Musulman Najeriya da ke niyyar zuwa Hajji.

Sheikh Tijjani ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a Kano, inda ya ce ya samu rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa gwamnatin tarayya ta amince da kashi 50 na tallafi ga Kiristoci da za su yi tafiya zuwa ƙasar Isra’ila sauke nasu faralin.

 Ya ce idan hakan gaskiya ne, bai dace a bar Musulmai a baya ba, tunda dukkansu ‘yan Najeriya ne.

Malamin ya bukaci ‘yan siyasa, musamman wakilai daga Arewacin Najeriya, da su sa baki don tabbatar da cewa gwamnati ta bayar da irin wannan tallafi ga maniyyatan Hajji. Ya yi gargadin cewa tsadar kuɗin Hajji na iya hana talakawa da dama samun damar zuwa ibadar.

Wannan kiran na Sheikh Tijjani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta ƙorafi daga Musulman Najeriya kan yadda kuɗin aikin Hajji ke ƙaruwa, abin da ke kawo cikas ga shirin zuwa ga masu ƙaramin ƙarfi.

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!