Gwamna Abba Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ta Kano

0
15

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Barrister Sa’idu Yahaya a matsayin sabon shugaban hukumar karɓar koke-koke da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC).

An gudanar da rantsuwar a fadar gwamnatin jihar, karkashin jagorancin kwamishinan shari’a na Kano, Barrister Haruna Isa Dederi.

Tun da farko, gwamnan ya tura sunan Yahaya zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da shi akan muƙamin.

 Yahaya ƙwararren masani ne a fannin yaki da cin hanci, wanda ya shafe fiye da shekaru 18 yana aiki a hukumar ICPC inda ya kware wajen bincike da gano kadarorin da aka mallaka ta hanyar rashawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here