Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kama manyan jami’an hukumar aikin hajji ta akan zargin wawure kuɗin hukumar.
Ma’aikatan da aka kama sune Aliu Abdulrazak, da Aminu Y. Muhammed, bisa zargin karkatar da wasu kuɗaɗe daga aikin Hajjin bana.
Rahotanni sun nuna cewa manyan jami’an sun amsa gayyatar EFCC ne, daga bisani aka tsare su bayan rashin mayar da kuɗin da ake zargin an karkatar. Har zuwa daren jiya suna tsare a hannun EFCC.
Majiyoyi sun ce ana kuma binciken su kan wani tsohon al’amari na karkatar da kuɗi tun lokacin shugabancin tsohon shugaban hukumar, Ahmad Jalal Arabi. Sai dai har yanzu babu adadin kuɗin da aka tantance da cewa an kwashe, domin an ce kuɗin sun haɗa da Naira, Riyal da Dalar Amurka.
NAHCON a wata sanarwa ta ce tana aiki tare da hukumomin gwamnati musamman na yaki da cin hanci, tare da tabbatar da gaskiya da bin doka a ayyukan ta.
Hukumar ta yi kira da a guji yada jita-jita a kan lamarin har sai an kammala bincike.