An samu ambaliyar ruwa a kasuwar Sharada a jihar Kano

0
15
Kano

’Yan kasuwa a kasuwar Sharada da ke cikin karamar hukumar birnin Kano, sun koka kan yadda rashin magudanan ruwa ke jawo musu ambaliya duk lokacin da aka yi ruwan sama.

Wani ɗan kasuwar, Alhaji Kabiru, da aka fi sani da Kabiru Na Mu, ya bayyana cewa sashen siyar da kayan abinci shi ne mafi shahara a kasuwar, kuma shi ne ke fuskantar mummunar matsala ta ambaliya a duk lokacin ruwan sama. Ya roƙi gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da shugaban ƙaramar hukumar birni, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, da su shigo cikin lamarin ta hanyar cike ramuka da gina magudanan ruwa.

Shi ma sakataren kuɗi na kasuwar, Malam Anas Idris, ya ce ban da matsalar ambaliya akwai buƙatar gwamnati ta sanya ƙofofi a bakin shiga da fita na kasuwar domin ƙarfafa tsaro, kasancewar harkokin kasuwanci na ci gaba gudana har cikin dare. 

Shugaban kwamitin rikon kasuwar, Alhaji Sa’idu Uba Ibrahim, yayi fatan cewa gwamnati za ta yi duba ta kawo sauƙi ga matsalolin. Ya ce duk da ƙoƙarin da suke yi wajen gyara wasu sassan kasuwar, musamman sashen kayan abinci, matsalar ta fi ƙarfin ikon su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here