Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 20, karkashin jagorancin Mai Shari’a Musa Ahmad, ta yanke wa wani matashi mai suna Halifa Usman Sheka hukuncin daurin shekara guda a gidan gyaran hali.
Kotun ta samu Halifa da laifin aikata fashi da makami a unguwar Gurun Gawa da ke Karamar Hukumar Kumbotso tun a shekarar 2022.
Rahotanni sun nuna cewa, Halifa ya kai hari a shagon wata mata mai suna Hadiza Abdulrazak, inda ya yi mata fashi da makami tare da jikkata ta ta hanyar yankar hannun ta.
A yayin yanke hukunci, Mai Shari’a Musa Ahmad ya ce kotu ta gamsu da shaidun da lauyan gwamnatin jihar Kano, Barista Ibrahim Arif Garba, ya gabatar.
Sai dai lauyan da ke kare shi, Barista M. H. Ma’aruf, ya nemi sassauci ga wanda ake kara.
Daga karshe kotun ta yanke masa hukuncin shekara daya a gidan gyaran hali, tana mai la’akari da cewa matashin ya riga ya shafe kusan shekaru uku a tsare kafin kammala shari’ar.