Masana sun bayyana cewa cutar koda sau da yawa tana farawa ba tare da alamomi ba, amma wasu dabi’u na yau da kullum suna iya haifar da ita.
Ga wasu daga ciki:
1. Yawan cin gishiri – na ƙara hawan jini da matsa wa koda yin aiki fiye da kima.
2. Rashin shan ruwa isasshe – yana rage karfin koda wajen tace datti.
3. Shan taba da barasa – suna lalata jijiyoyi, suna ƙara haɗarin ciwon koda.
4. Rashin isasshen barci – yana dagula aikin jiki da koda.
5. Zaman banza ba tare da motsa jiki ba – yana jawo kiba, hawan jini da ciwon sukari.
6. Rashin yin gwaje-gwajen lafiya – na sa cututtuka su cigaba ba tare da gano su da wuri ba.
Masana lafiya sun ja hankalin jama’a da cewa kare koda da hana cutar ya fi sauƙi da araha fiye da magance ta bayan ta bayyana a jikin mutum.