Gwamnatin tarayya zata yi ƙarin albashin masu riƙe da muƙaman siyasa

0
12

Hukumar Tattarawa da Rabon tattalin arzikin ƙasa (RMAFC) ta bayyana shirinta na sake duba albashin manyan jami’an siyasa a Najeriya, tana mai cewa albashin da suke samu yanzu bai dace da yanayin matsalolin tattalin arzikin ƙasa ba.

Shugaban hukumar, Mohammed Shehu, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Litinin. Ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu na karɓar albashi na Naira miliyan 1.5 a wata, yayin da ministoci ke karɓar ƙasa da Naira miliyan 1, albashin da bai canza tun daga shekarar 2008.

“Shehu ya ce, ana biyan shugaban ƙasar Najeriya Naira miliyan 1.5m a wata, alhali ƙasar tana da mutane sama da miliyan 200. Wannan abin dariya ne, inji shi.

Ya ƙara da cewa, ba za ka iya biyan minista ƙasa da Naira miliyan 1, tun daga 2008 ba ka kuma yi tsammanin zai yi aiki da ƙwazo ba tare da shiga wasu al’amura na gefe ba. Hakan ba daidai ba ne, musamman idan aka kwatanta da yadda ake biyan gwamnan CBN ko darakta-janar sau goma fiye da shugaban ƙasa, ko sau ashirin fiye da babban Lauyan Ƙasa.”

Sai dai kungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta yi hanzari wajen sukar wannan shirin, inda ta ce hakan zai ƙara haɓaka banbancin da ke tsakanin masu mulki da talakawa, musamman ganin cewa akwai ƙarin fa’idoji da dama da jami’an gwamnati ke amfana da su ba tare da an bayyana ba.

Shugaban hukumar RMAFC ya jaddada cewa ba aikin hukumar ba ne sanar da mafi ƙarancin albashi na ma’aikatan gwamnati ba, illa dai tsarin albashin jami’an siyasa, na shari’a da na majalisa wanda kundin tsarin mulki ya dora musu alhakin tsara shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here