Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya musanta jita-jitar da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa yana fama da rashin lafiya mai tsanani a birnin London.
Akpabio ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 4 na asubahin ranar Litinin, bayan dawowa daga London. An tarbe shi a sashen shugabanni na filin jirgin ta hannun wasu sanatoci, hadimai da magoya baya.
Rahotanni a kafafen sada zumunta sun ruwaito cewa shugaban majalisar dattawan na kwance a asibiti, lamarin da ya bayyana a matsayin ƙarya tsagwaronta.
Lafiyata ƙalau take. Na tsaya a London ne kawai don ɗan hutu na ɗan lokaci,” in ji shi yayin da yake zantawa da manema labarai a filin jirgin.
Tun kafin wannan hutu, Akpabio ya halarci taron shugabannin majalisun dokoki na duniya karo na shida a Geneva, Switzerland, daga ranar 29 zuwa 31 ga watan Yuli.