Tsohon ɗan majalisar tarayya, Sanata Shehu Sani, ya shawarci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da kada ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Sani ya bayyana hakan ne a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, inda ya ce jam’iyyar PDP da Jonathan ya yi amfani da ita wajen lashe zaɓe a 2011 yanzu ta rabu gida biyu, ba kamar da ba.
A cewarsa ”kowane lokaci idan zaɓe ya gabato, ana ambato sunan Jonathan, amma shawarar da nake bashi ita ce kada ya sake tsayawa. Dalili kuwa shi ne PDP ɗin da ya sani a baya ba ita ce yanzu ba. A yau wasu daga cikin shugabannin PDP musamman a yankin kudu maso yamma na mara wa Shugaba Tinubu baya, yayin da wasu kuma ke cikin haɗaka da shi. Saboda haka bai kamata ya ɓata lokacinsa ba.”
Sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a majalisar tarayya ta takwas ya ƙara da cewa waɗanda ke cikin haɗakar siyasar yanzu ba su da bambanci da shugaba Bola Tinubu a akida.
Ya kuma yi gargadi da cewa, “Dimokaradiyya tana buƙatar adawa mai ƙarfi wacce za ta samar da madadin tsari da mulki. Amma idan manufarsu kawai ta tsaya ne a cire Tinubu ba tare da wata sabuwar hanyar mulki ko tsari ba, to hakan na nufin babu wata manufa ko shiri da suke da shi.”