Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Kashe Mutane da Dama a Sokoto

0
1

An shiga jimami a Jihar Sokoto a ranar Lahadi bayan wani jirgin ruwa ya kife a yankin Kojiyo, na Karamar Hukumar Goronyo, lamarin da ake zaton ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, yayin da wasu suka ɓace.

Jirgin ruwan, wanda ke ɗauke da fasinjoji masu yawa masu zuwa kasuwar Goronyo, ya nutse a tsakiyar ruwa, lamarin da ya jawo asarar rayuka da tashin hankali a yankin.

Wani ganau mai suna Abubakar ya shaida cewa mutane da dama sun rasu, yayin da har zuwa daren Lahadi ake ci gaba da aikin ceto da neman waɗanda suka ɓace.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta bayyana cewa ta tura tawagar ta, ta jami’an ceto daga ofishin Sokoto domin taimakawa. Darakta Janar ta hukumar, Zubaida Umar, ta ce an samu rahoto cewa jirgin ruwan da ya kife na ɗauke da fasinjoji fiye da 50 a lokacin da hatsarin ya faru.

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!