Gwamnatin tarayya ta amince da kashe wasu kuɗaɗe domin inganta samar da lantarki a sassan ƙasar nan, inda za’a kashe naira biliyan 13 da za a yi amfani da su wajen aikin inganta lantarkin a jihohin Legas da Ogun.
Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana hakan bayan kammala zaman majalisar zartarwar tarayya a makon da muke ban kwana da shi, inda ya ce an amince da daftari huɗu na musamman domin inganta bangaren samar da wutar lantarki.
Daftari na farko, ya shafi cigaba da biyan diyya ga mutanen da aka karɓi kadarori ko gine-ginensu domin aikin shimfiɗa layukan lantarki.
Adelabu ya ƙara da cewa, majalisa ta amince da biyan diyya ta naira biliyan 13 a ƙarƙashin aikin Layin lantarkin Lagos, wanda za a biya daga bashin dala miliyan 238 da Japan za ta bayar.
Sauran daftari ukun kuma sun shafi amincewa da shigo da sabbin na’urorin rarraba wutar lantarki domin maye gurbin tsofaffi da ke manyan layukan rarraba lantarki.