Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin kayayyakin masarufi ta sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22% a watan Yuni, abin da ya nuna karo na huɗu da aka samu raguwar hauhawar farashin a bana.
Idan aka kwatanta da Yuli 2024, an samu raguwa da kashi 11.52% daga kashi 33.40% na bara, duk da cewa a ma’aunin wata zuwa wata, hauhawar farashi ya tashi zuwa kashi 1.99% daga 1.68% a Yuni.
NBS ta bayyana cewa abinci da abin sha, gidajen cin abinci da masauki, da sufuri ne suka fi samun tashin farashi a watan Yuli.
Farashin abinci ya kai kashi 22.74% a shekara guda, ya ƙaru daga 21.97% a watan Yuni, amma ya ragu da kashi 16.79% idan aka kwatanta da bara (39.53%).
A ma’aunin wata zuwa wata, farashin abinci ya ragu zuwa kashi 3.12% saboda saukar farashin man girki, wake, shinkafa ta gida, garin masara, dawa, gero da sauransu.