Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu

0
1

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya ce gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i guda 9, da suka haɗar da Jami’ar Tazkiyah (Kaduna), Leadership (Abuja), Jimoh Babalola (Kwara), Bridget (Imo), Greenland (Jigawa), JEFAP (Neja), Azione Verde (Imo), Unique Open (Legas), da American Open (Ogun).

Alausa ya bayyana cewa daga cikin buƙatu 551 na kafa sababbin jami’o’i da gwamnatin Tinubu ta gada, an tantance 79, sannan aka amince da waɗannan tara bayan cikakken bincike da tsauraran ka’idoji. 

Ya kuma ce wasu daga cikin jami’o’in sun shafe fiye da shekaru shida suna jiran izinin aiki duk da cewa an riga an gina su tare da zuba kuɗaɗe masu yawa a cikin su.

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!