Hukumar Kwastam ta bai wa Sojojin Najeriya jirage marasa matuka 86

0
132

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta mika wa Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya jirage marasa matuka guda 86 da ta kwace a hannun masu fasakwauri.

Hukumar Kwastam ta kwace jiragen ne saboda rashin lasisin da ya wajaba su mallaka, wanda kuma Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, ne ke bayarwa.

Da yake mika wa rundunar jiragen, Kwanturola-Janar na hukumar, Hamid Ali, ya ce samun lasisin na daga cikin sharuddan da doka ta gindaya na mallakar irin jiragen da wasu abubuwa.

Hamid Ali, wanda Konturolan Kwastam na Abuja, Suleiman Bomoi ya wakilta, ya ce, hukumar ta samu izinin kotu na kwace jiragen a kafin mika su ga rundunar bayan an kotu ta mallaka su ga Gwamnatin Tarayya.

“Mun lalata jiragen mayan mun kama su a Filin Jiragen Sama da ke Abuja, sannan muka samu umarnin kotu na lalata su.

“Kwanturola-Janar Hukumar Kwastam, Hamid Ali ya umarce ni in mika su 86 ga Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, a wani bangare na hadin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaro.”

Da yake karbar jiragen a madadin Babban Hafsan Sojin Ruwa ta Najeriya, Bais Admiral Awwal Gambo, Shugaban Sashen Horo da Ayyuka na Hedikwatar Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya, Riya Admiral Solomon Agada, ya ce za rundunar za ta yi amfani da jiragen yadda ya kamata wajen tsaron kasa.

Ya bayyana cewa mika musu jiragen na daga cikin hadin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaro domin samar da aminci a Najeriya.

Ya ce, “A madadin Rundunar Sojoin Ruwa ta Najeriya, na karbi wadannen jirage marasa matuka guda 86, wadanda Hukumar Kwastam ta kama, kotu ta mallaka wa Gwamnatin Tarayya, wadanda yanzu aka mika wa rundunarmu.

“Ina ba da tabbacin cewa Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya za ta yi amfani da su yadda ya kamata wajen samar da tsaro.

“Babban Hafsanmu yana godiya ga Kwanturola-Janar da Hukumar saboda wannan abu da ya yi na hadin gwiwa, kuma za mu ci gaba da hidimta wa kasarmu,” in ji shi.

AMINYA