Majalisar Kano ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Rano

0
15

Majalisar dokokin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban karamar hukumar Rano, Naziru Ya’u, na tsawon watanni uku.

Rahotanni sun bayyana cewa an dauki wannan mataki ne saboda zargin sayar da tsohuwar kasuwar Rano.

Bugu da kari, ana zargin cewa ya sayar da takin zamani na noma da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rabawa kananan hukumomi a watan Yuli da ya gabata, inda kowace karamar hukuma ta samu tirela uku dauke da buhunan taki 600 kowacce.

Wata majiya daga Majalisar ta shaida cewa ana ci gaba da tattaunawa kan matakin da za a dauka a kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here