Soludo: Shugaba Tinubu na cikin koshin lafiya, babu abin da ke damun sa

0
49

Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na cikin koshin lafiya, sabanin jita-jitar da ke yawo a kwanakin nan.

Soludo ya bayyana haka ne ranar Litinin bayan ganawar da ya yi da shugaban kasa a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja. Ya ce Tinubu yana cikin shirin aiki yadda ya kamata, kuma yana ci gaba da ganawa da jama’a.

A ’yan kwanakin baya, an yi ta rade-radin cewa shugaban kasa na fama da rashin lafiya, lamarin da ya biyo bayan kusan mako guda da ba a ji daga gare shi ko kuma ganin sa a taruka ba.

“Shugaban kasa na cikin koshin lafiya sosai, kuma ganawar da muka yi ta kasance mai kyau,” in ji Soludo.

Baya ga Gwamna Soludo, sauran manyan jami’an gwamnati da suka ziyarci Shugaba Tinubu a ranar Litinin sun haɗa da Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, Sanatan Nasarawa ta Yamma, Aliyu Wadada, da Ministan Kudi, Wale Edun.

Soludo, wanda ke neman wa’adi na biyu a zaben gwamnan Anambra da za a gudanar ranar 8 ga Nuwamba, ya bukaci ’yan Najeriya da su mara wa Tinubu baya, yana bayyana shi a matsayin jagoran cigaban dimokuradiyya da tattalin arzikin ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here