Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sudan ta fitar da Nijeriya daga gasar CHAN bayan ta lallasa ta da ci 4-0 a wasan maraicen Talata, wanda ake bugawa tsakanin ‘yan wasan da ke taka leda a ƙasashen Afirka kawai.
Wasan shi ne na biyu da Nijeriya ta buga a Rukunin D, wanda aka yi a Filin Wasa na Amaan da ke birnin Zanzibar, Tanzania.
A makon jiya, Senegal ma ta doke Nijeriya da ci 1-0 a gasar ta CHAN 2024.
Sakamakon wannan nasara, Sudan na gab da tsallakewa zuwa mataki na gaba a gasar.