Najeriya da Isra’ila Za Su Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro

0
13

Kasashen Najeriya da Isra’ila sun jaddada aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro, musamman wajen yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗaɗen tsaro da horaswa ta musamman.

Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da takwararta ta Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz, ne suka bayyana haka bayan wani  taron da suka gudanar a Abuja.

Sun yi kira ga ƙasashen duniya su haɗa kai wajen dakile ta’addanci da hanyoyin samun kuɗaɗen da ake amfani da su a wajen yan ta’addan. Haka kuma sun amince su faɗaɗa haɗin kai a fannonin fasaha, kula da iyakoki, noma, yawon buɗe ido da hulɗar jakadanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here