Rundunar ‘Yan Sanda Kano zata fara kama yara masu tuƙa Adaidaita sahu

0
12

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi gargaɗi kan yadda yara ƙanana ke tuƙa babur mai ƙafa uku da aka fi sani da Adaadaita Sahu a birnin Kano.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, rundunar ta bayyana damuwarta game da yadda wannan dabi’a ke ƙara yawaita, tana mai cewa hakan na jefa rayukan jama’a cikin haɗari.

Sanarwar ta ce a watan Agusta kaɗai, an samu manyan haɗurra 16 sakamakon irin wannan tuƙi, wanda ya jikkata mutane da dama tare da jawo asarar dukiya mai yawa.

‘Yan sandan sun shawarci jama’a su riƙa bin ƙa’idojin tuƙi da kuma mutunta fitilun kan hanya (traffic lights), tare da yin biyayya ga dokoki.

Haka kuma rundunar ta sha alwashin cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kamawa da hukunta duk wanda ya karya doka, domin tabbatar da tsaro da kare lafiyar al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here