Kwamitin tsaron unguwar Sharaɗa ya sanar da dokoki guda 29, ciki har da haramta yin zance a cikin mota mai duhu, da kuma hana tattaunawar saurayi da budurwa bayan ƙarfe 10 na dare.
Wannan mataki na daga cikin shirin ƙara tabbatar da tsaro a yankin.
Dagacin Sharaɗa, Alhaji Ilyasu Mu’azu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan inda ya ce dokokin sun samu amincewar shugabannin unguwanni, dattawan yankin, da kuma shugaban ƙaramar hukumar Birni da kewaye, Salim Hashim.
Shugaban ƙaramar hukumar, Salim Hashim, ya yi kira ga al’ummar Sharaɗa da su bayar da cikakkiyar gudunmawa domin ganin an aiwatar da dokokin, yana mai cewa hakan zai ƙara tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.