Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai mummunan hari a wani masallaci da ke kauyen Marnona, a karamar hukumar Wurno dake jihar Sokoto, da safiyar Talata yayin sallar Asuba.
Shaidun gani da ido sun ce maharan sun rika harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya jefa masu ibada cikin firgici. Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama.
Shugaban jam’iyyar APC a jihar Sokoto, Rt. Hon. Isah Sadeeq Achida, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin da rashin mani.
Ya ce kai wa masu ibada hari a wajen ibada alamar rashin ɗabi’a ce babba a tsakanin maharan.
Achida ya roƙi su haɗa kai wajen yaki da ‘yan bindiga, yana jaddada cewa wannan hari ba wai kawai ya ci zarafin rayuka bane, har ma da barna ga addini da dabi’un haɗin kan al’umma.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar tare da jami’an tsaro na ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen lamarin da kuma kamo masu laifin.
Har yanzu, rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta fitar da sanarwa kan adadin waɗanda suka mutu ko yiwuwar sace mutane a wannan hari ba.