Jihohi na cikin barazanar fuskantar karin ambaliya – Nimet

0
134

Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya ta ce akwai yiwuwar karin jihohi su fuskanci ambaliyar ruwa a cikin kwanaki masu zuwa, musamman ma yankin Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Gabas da kuma Kudancin kasar.

Babban darektan hukumar, farfesa Mansur Bako Matazu, shi ya bayyana hakan a wani taron wayar da kai kan yanayi.

Babban darektan hukumar ya ce a cikin kwanaki masu zuwa, za a samu mamakon ruwan sama wanda zai iya janyo karin ambaliya ganin kuma an bude madatsun ruwa.

Jihohin Benue da Kogi na fuskantar gagarumar ambaliya wanda rabon aga hakan tun 2012, inda ambaliyar ta janyo asarar rayuka da kuma na dukiyoyi da ya kai na biliyoyin kudi.