Sarkin Kano na 15 ya miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnatin Ghana 

0
28

Sarkin Kano, na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, ya aike da sakon ta’aziyya ga gwamnatin Ghana, da kuma al’ummar kasar, biyo bayan mummunan hatsarin jirgin sama na soji da ya yi sanadin mutuwar mutane takwas a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa wannan rashin ba wai na Ghana kadai bane, har ma da Najeriya da dukan kasashen Yammacin Afirka.

“Ina mika ta’aziyya cikin tsananin jimami ga gwamnatin Ghana, iyalai, da al’ummar kasar baki daya kan rasuwar mutane takwas a hatsarin jirgin soji. Lallai wannan babban rashi ne ga Ghana da kuma mu ‘yan’uwanku a Najeriya,” inji shi.

Ya yi addu’ar Allah Ya jikan mamatan, ya kuma bawa iyalansu da kasar Ghana hakurin jure wannan babban rashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here