Abdulmunin Jibril Kofa ya sake ganawa da shugaban ƙasa Tinubu

0
27

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sake ganawar sirri da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar sa.

Wannan shi ne karo na biyu cikin ƙasa da makonni biyu da ɗan majalisar ya kai wa shugaban ƙasa ziyara irin wannan.

Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta gudana da yammacin Lahadi, inda ya ɗauki kusan sa’o’i biyu tare da shugaban.

Ko da yake Jibrin bai bayyana abin da suka tattauna ba, wasu majiyoyi sun ce batun na iya zama yana da nasaba da dangantakar tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da Shugaban ƙasa Tinubu.

Da manema labarai na fadar shugaban ƙasa suka tambaye shi manufar wannan ganawa ta biyu, ya ƙi yin karin bayani.

A ganawar da ya yi kwanaki goma a baya, Jibrin ya bayyana cewa tattaunawar ta ta’allaka ne kan “batutuwan cigaban ƙasa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here