Gwamnatin tarayya ta gargadi Kano da sauran jihohin arewa akan ambaliya

0
23

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin samun ambaliya a jihohi 15 daga cikin jihohi 19 na Arewacin ƙasar nan, inda ta bukaci al’umma da hukumomi su dauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi.

Wannan gargadi ya fito ne a ranar Lahadi daga Cibiyar Gargadin Ambaliya ta Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, a cikin wata sanarwa da Malam Usman Abdullahi Bokani, Daraktan Sashen Kula da Ƙasa, Ambaliya da Yankunan Gabar Ruwa, ya sanya wa hannu. Ya bayyana cewa jihohin Adamawa, Bauchi, Nasarawa, Kaduna, Katsina da Kebbi na cikin jerin wuraren da ke cikin haɗari sosai.

Sauran jihohin da aka sanya a cikin gargadin sun haɗa da Kano, Niger, Taraba, Jigawa, Yobe, Zamfara, Sokoto, Borno da Kwara. Haka kuma, wasu garuruwa kamar Jimeta, Mubi, Keffi, Kafanchan, Birnin Kebbi, Minna, Gusau da Sokoto na cikin wuraren da ake ganin za su iya fuskantar ambaliya mai tsanani. A Kebbi kuwa, an lissafa garuruwa da dama kamar Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega da Birnin Kebbi a matsayin wuraren da ya kamata a kula da su sosai.

Malam Bokani ya roƙi mazauna yankuna, hukumomin kananan hukumomi da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki su dauki matakan kariya tun kafin faruwar ambaliyar, tare da samar da rahotanni cikin lokaci don a samu damar daukar matakan gaggawa idan ambaliya ta faru.

Wannan gargadi ya biyo bayan wani irin irin gargadin da aka fitar a watan da ya gabata ga jihohi 11, lamarin da ke nuna cewa akwai buƙatar ci gaba da kula da shirin kare kai a yankin Arewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here