Wasu manyan motocin dakon mai biyu sun yi hatsari a safiyar Litinin a yankin Ɗan Magaji, dake ƙaramar hukumar Zariya, a jihar Kaduna, lamarin da ya haddasa tashin gobara mai tsanani.
Shaidu sun bayyana cewa hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 8:30 na safe, a kusa da Makarantar Rochas Foundation, kan titin Kaduna zuwa Kano daga Kwangila zuwa Ɗan Magaji.
Hatsarin ya haɗa da manyan motocin mai biyu da motoci ƙirar Golf guda biyu ɗauke da fasinjoji.
Tankokin sun yi bindiga, wanda ya jawo tashin gobara mai ƙarfi, tare da hayaƙi mai.
Jami’an ceto da tsaro sun rufe hanyar, tare da gargadin direbobi da su kauce wa wucewa ta wurin, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da kwashe gawarwakin waɗanda lamarin ya rutsa da su.