Gwamnatin Adamawa ta karyata zargin rabawa mutane lalataccen abinci

0
16

Gwamnatin Jihar Adamawa ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa kayan abincin da aka rabawa waɗanda ambaliya ta shafa a ranar Asabar da ta gabata a Kwalejin Mustapha da ke Karamar Hukumar Yola ta Kudu, sun kasance waɗanda lokacin amfani da su ya kare.

A wata hira da ta yi da jaridar PUNCH a ranar Lahadi, Sakatariyar Hukumar bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA), Celine Laori, ta bayyana rahoton da ke yawo a yanar gizo a matsayin wanda ba na gaskiya ba, tana mai zargin wasu ‘yan adawa da ƙoƙarin bata sunan Gwamna Ahmadu Fintiri.

Ta ce duk da yadda gwamnatin yanzu ta bai wa kowa dama wajen naɗe-naɗen mukamai da rarraba ayyukan ci gaba a kananan hukumomi 21 na jihar, akwai wasu ‘yan siyasa da suka sha kaye a zaɓe suna nuna ƙiyayya ta hanyar da ba ta dace ba. Laori ta jaddada cewa tun bayan dawowar dimokuraɗiyya a 1999, babu wata gwamnati a Adamawa da ta kai ko rabin abin da Fintiri ya cimma cikin shekaru biyar na mulkinsa.

A cewarta, a matsayinta na likita, abin mamaki ne kuma abin takaici a zarge ta da amincewa a raba abinci da ya ƙare ga talakawa.

A ranar Asabar, Mataimakiyar Gwamna, Farfesa Kaletapwa Farauta, ta raba nau’ikan kayan abinci ga gidaje 4,000 da ambaliyar da ta faru a watan da ya gabata ta shafa a Yola ta Kudu. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here