Sojoji sun kashe wani kwamandan ƴan ta’adda mai suna Amirul Fiya wanda ake kuma kira Abu Nazir, tare da wasu mayakansa a karamar hukumar Balge, jihar Borno, bayan sun dakile wani hari da aka kai musu.
Sanarwar da Mukaddashiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar Sojin Najeriya, Laftanar Kanal Appolonia Anele, ta fitar a ranar Lahadi ta bayyana cewa an gano gawar kwamandan tare da wasu ‘yan ta’adda biyu, kana an kwato bindiga AK-47, bama-bamai guda biyu na roka, da wasu kayan yaƙi.
A cewarta, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga Agusta 2025 lokacin da dakarun Bataliya ta 3 dake Rann Kala, suka mayar da martani kan harin ISWAP/JAS.
Bayan haka, alamu sun nuna wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere da raunuka.
A Zamfara kuwa, dakarun sun yi nasarar ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Gusau zuwa Kaura Namoda, bayan samun sahihin bayani kan ayyukan ‘yan ta’adda a yankin Unguwar Sarkin Musulmi, karamar hukumar Kaura Namoda.
Tuni an mayar da waɗanda aka ceto zuwa ga iyalansu.