NDLEA ta kama faston kan safarar miyagun ƙwayoyi

0
44

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wani babban faston majami’ar The Turn of Mercy Church, Adefolusho Olasele, bisa zargin hannu a safarar miyagun ƙwayoyi daga Ghana zuwa Najeriya.

An cafke faston ne ranar Lahadi, 3 ga Agusta 2025, a cocinsa da ke Okun Ajah, jihar Legas, bayan watanni yana gujewa hukumomi. Rahoton hukumar ya bayyana cewa jami’an NDLEA sun jira har sai da ya kammala wa’azi kafin su kama shi a yayin da yake barin harabar cocin.

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce Olasele ya tsere zuwa Ghana a watan Yuni, bayan an alaƙanta shi da wasu ganyen wiwi mai nauyin kilo 200 da aka kama a bakin ruwa na Okun Ajah ranar 4 ga Yuni, da kuma wani adadi da aka samu a cikin motarsa.

Babafemi ya ƙara da cewa, faston ya amsa cewa yana safarar ƙwayoyi ta ruwa daga Ghana zuwa Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here