Zan iya kayar da Tinubu a 2027 idan na samu tikitin ADC–Ameachi

0
11

Tsohon Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, ya ce zai iya doke Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 idan ya samu tikitin jam’iyyar ADC.

Amaechi, wanda ya shaida hakan a wata tattaunawa a shafin X, ya ce bai taɓa shiga maguɗin zaɓe ba kuma ya ƙi shiga duk wani kwamitin shirya zaɓen APC saboda ya san irin tattaunawar da ake yi a ciki.

Ya zargi wasu gwamnonin jihohi da karkatar da kuɗin gwamnati domin maguɗin zaɓe, tare da alƙawarin kawo ƙarshen hakan idan ya zama shugaban ƙasa.

Amaechi ya kuma amince cewa Peter Obi na jam’iyyar Labour Party ya yi nasara a jihar Rivers a zaben 2023, amma sakamakon da aka fitar ya bambanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here